Iná Néman Mulki Né Domìn Gína Jìhar Kanó Da Mutanenta - Nasíru Gawuna
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin Inuwar Jamiyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa ba buƙatarsa ce ta sa shi fitowa neman gwamnan Jihar Kano ba. Son sa da Jihar Kano da burin da ya ke da shi na son gina Jihar ta zama tamkar wata sabuwar Duniya da samarwa matasa ayyukan yi su ne su ka sanya shi neman mulkin.
Dr. Gawuna ya kuma ja hankalin mabiya da magoya baya da su gudanar da yaƙin neman zaɓe da harkokin siyasa cikin mutunci. "Ina kiran mago bayanmu da su guji aibata ƴan adawa da munanan kalamai ko ƙage da sharri domin ba tarbiyar siyasarmu ba ce, a mutunta kowa ayi siyasa ba gaba".
Daga nan ya kuma bayyana cewa mulki na Allah ne, kuma agunsa ya ke nema, in ya samu Alhamdulillah, in ya rasa ma Alhamdulillah, domin babu kuskure a lamarin Allah ya kan hana bawa wani abu domin hakan ya zamto shi ne mafi alkhairi a gare shi.
Haka zalika ya cigaba da cewa: "Zaɓe na zuwa, Ina son al'umma su duba tarihina, idan har na cancanta to su jefa mun quri'unsu, ina kuma fatan Allah Ya sa na zamto ni ne mafi alkhairi ga Jihar da al'ummar".
"Ina da rubutaccen tsari da cikakken kundin gudanarwa da na tsara wanda zan yi amfani da shi wajen raya Kano dazarar al'umma sun zaɓe mu an rantsar da mu. Na yi alƙawarin tallafa matasa da samar musu abubuwan dogaro da kai. Zan inganta masarautunmu guda 5, zan ƙara ɗaga darajarsu su zamto daidai da manyan masarautun da ake ji da su a ko'ina. Zan tallafawa ɗalibai a kowane fanni mu samu masana da ƙwararru batare da an bar mu a baya ba".
Dr. Nasiru Gawuna, ya cigaba da cewa: Na zagaya ƙasashen Duniya da dama tun shekarar 2012, na ga tsare-tsare na cigaba waɗanda in mu ka yi amfani da su za mu ɗaga daraja da cigaban Jihar Kano. Na ƙudiri aniyar maida Jihar Kano wata babbar farfajiya wacce za a gani ayi alfahari da ita". -Nasiru Gawuna.

Comments
Post a Comment