Wani Matashi Ya Nutse A Rijiya Wajen Kokarin Ciro Bokiti
👇👇👇
Wani matashi mai shekara 27 a duniya ya nutse a rijiya yayin kokarin ciro bokitin da ya fada cikin rijiya.
Lamarin dai ya auku ne a kauyen Alaja cikin karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
A cewar majiyar, mamacin yaron mota ne sannan da shi da ogan sa direban babbar mota suna kan hanyar su ta zuwa wani waje ne a jihar a ranar Asabar, 18 ga watan Fabrairun 2023.
Kawai suna tsaka da tafiya sai motar ta lalace musu a kusa da karshen mahadar Powerline/Moniya na sabuwar hanyar Ibadan zuwa Oy8o.

Comments
Post a Comment