Yadda ƳanSanda Suka Saki Tinkiya Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi A Borno
👇👇👇
ƳanSanda Suka Saki Tinkiya Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi A Yan Sanda Sun Saki Tinkiya Da Aka Kama Daa Laifin Cin Bushasshen Kifi A Borno
Rundunar yansanda a jihar Borno ta saki Tinkiyar da aka damke kan laifin cinye bushasshen Kifin
wani dan kasuwa, Malam Yusuf Ibrahim, a unguwar Bulabulin Maiduguri, jihar Borno.Mai tinkiyar, Luba Mohammed, ya bukaci dattawan unguwa su tayashi baiwa Mai Kifi Ibrahim hakuri.
Shigar da Tinkiya Kara
Ibrahim, mai sayar da kifin da ya kai karar Tinkiyar caji Ofis ya bayyanawa manema labarai cewa dattawan unguwa sun bashi hakuri kuma ya hakura, kamar yadda shafin internet na jaridar Legit.ng ya wallafa.
Ibrahim ya bayyana cewa ya dade yana yiwa Luba gargadi bisa wannan asara da Tinkiyarsa ke janyo masa, kamar yadda rahoton DailyTrust ya bayyana.
A cewarsa, mai tinkiyar bai dau wani mataki kan hakan ba kuma ya sa ya yanke shawarar kai kara wajen hukumar.

Comments
Post a Comment